IQNA

23:55 - May 14, 2019
Lambar Labari: 3483639
Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci a kawo karshen kyamatar al'ummomi saboda addininsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da ya kai wata ziyara a jiya a wani masallaci a kasar New Zealand da aka kashi mutane 40 a cikinsa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, dole ne  kawo karshen nuna kiyayya ga al’ummomi a fadin duniya.

Ya ce yana da muhimamnci a karfafa tattaunawa tsakanin al’ummomi da addinai, domin kara samun fahimtar juna da kuma girmama ra’ayi da akida da mahangar juna, wanda hakan shi ne zai kawo zaman lafiya da karfafa kauna da amince a tsakanin al’ummomin duniya.

Ya kara da cewa, yana zimmar ganin an samar da wani shiri a mataki na kasa da kasa, dangane da tattaunawa tsakanin jagororin addinai na duniya domin magance wannan matsala, wadda take barazana ga zaman lafiyar duniya a halin yanzu.

 

 

 

3811582

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: