IQNA

23:55 - May 18, 2019
Lambar Labari: 3483652
Rahotanni daga birnin Abuja na cewa, a daren jiya magoya bayan harkar musulunci sun gudanar da jerin gwano domin yin kira da a saki sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi tsawon shekaru fiye da uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Wasu kafofin yada labarai sun ambaci cewa, jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa masu jerin gwanon, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatarwa kafofin yada labarai hakan, kuma suka ce ba su yi harbi da bindiga ba, kuma an ji harbin ne a lokacin da wasu sojoji suke wucewa ta wurin.

Rahotannin sun kara da cewa, wasu daga cikin masu gudaar da jerin gwanon sun samu raunuka sakamakon harbin, amma babu rahotanni kan ko wasu sun rasa rayukansu.

Tunakarshen shekara ta 2015 ce dai jami’an sojin Najeriya suka kama sheikh Ibrahim Zakzaky tare da mai dakinsa, bayan kai harin da suka yi a kan gidansa da ke unguwar Gyallesu a Zaria, inda suka kashe adadi mai yawa na mabiyansa, tare da kona gidansa da kuma wasu cibiyoyi na Harkar musulunci a Zaria.

3812647

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، Abuja ، Zakzaky
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: