IQNA

23:55 - May 21, 2019
Lambar Labari: 3483661
Tattaunawa tsakanin sojoji masu mulkin kasar Sudan ya kasa kaiwa ga natija kwanaki biyu a jere kamar yadda majalisar sojojin kasar ta bayyana.

Kamfanin dillancin labaran iqna tashar Russia Today ta bayar da cewa, duk da cewa sojojin sun yiwa tsohon shugaban kasar juyin mulki tun ranar sha daya ga watan Afrilu amma masu zanga-zanga day an adawa suna ganin hakan bai wadatarba sai sojojin sun mika mulki ga gwamnatin Farar Hula.

Majalisar sojojin ta kara da cewa zata ci gaba da tattaunawa da wakilan masu zanga-zangar da kuma jam’iyyun adawa har zuwa lokacinda za’a fahinci juna.

Mazau zanga-zangar dai sun mamaye haramar ma’aikatar tsaron kasar ta Sudan suna ci gaba da zaman dirshen a wurin har sai sojojin sun biya bukatunsu wadanda suka hada da kakkabe hannun sojoji a shugabancin kasar da kuma yi masu adalci a cikin wadanda aka kashe tun ranar sha tara  ga watan Disamba da ya gabata kafin juyin mulkin da aka yiwa tsohon shugaban kasar.

Mafi yawan jam’iyyun dai sun amince da gwamnatin rikon kwarya ta shekaru ukku amma kuma sun sami sabani da sojojin ne kan wa zai jagoranci gwamnatin da kuma zabubbukann da za’a gudanar a lokacin gwamnatin rikon kwaryan.

3813515

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sudan ، tattaunawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: