IQNA

Nasrullah: Yaki Da Yarejejniyar Karni Aikin Addini Ne

22:56 - June 01, 2019
Lambar Labari: 3483696
A jiya jumma’a da yamma ce shugaban kungiyar Huzbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya yi jawabi wanda aka watsi kan tsaye a tashoshin talabijin da dama a duk fadin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Hassan nasrullah jawabin nasa ya zo ne don raya ranar Qudus ta duniya wacce it ace ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan na ko wacce shekara, kamar yadda marigayi Imam Khomaini ® wanda ya assasa JMI ya ayyana.

A cikin jawabin nasa Sayyid Hassan Nasarallah, ya tabo batutuwa da dama daga ciki akwai batun gangar yakin da Amurka da kawayenta suke kadawa a kan Iran da kuma yankin gabas ta tsaikiya, inda ya bayyana cewa duk wani yakin da Amurka da kawayenta zasu kaiwa kasar Iran, to su kwana da sanin cewa yakin ba zai takaita a kan iyakokin kasar Iran ba.

Nasarrallah ya kara da cewa, yakin sai ya gama dukkan kasashen yankin sannan Amurka ta kwana da sanin cewa dukkan masalahonta a gabatar da tsakiya ba zasu tsira daga wutar yakin ba, daga cikin har da HKI.

Banda haka Nasarraka ya kara da cewa hatta sarakunan kasashen larabawa da suke ruruta wutar yakin, suma ba zasu tsira ba.

Har’ila yau shugabann kungiyar Hizbullah ya yaba da jawaban da shugaban kasar Iraqi Barham Salih ya gabatar a taron kasashen Larabawa na yankin Tekun farisa wanda shugaban kasar saudia ya bukaci a gudanar da shi a birnin Makka, a makon da ya gabata, inda ya nuna goyon bayansa ga Kasar Iran sannan ya yiwa kasashen larabawa kashedi kan takalar yaki da kasar Iran.

Sayyid Nasarral ya zargi tawagar kasar Lebanon a taron na Makka, da rashin bayyana hakikanin matsayin mutanen kasar a taron, ya ce wadanda suka wakili kasar Lebanon a taron na Makka sun wakilci kansu ne, amma ba ra’ayin mutanen kasar ba

Dangane da “Yerjejeniyar karni” kuma, wanda shugaban kasar Amurka donal trump yake son aiwatarwa dangane da matsalar al-ummar Palasdinu, sayyid Nasarallah ya yabawa al-ummar palasdinawa wacce gaba dayanta ta yi watsi da yerjejeniyar, sannan ya ce wajibimmu ne, a matsayimmu na mutane, musulmi da kuma larabawa, mu yi fada da wannan yerjejeniyar, har sai ta kasa kaiwa ga nasara.

Nasarallah ya kammala da cewa kasashen Amurka da HKI da kuma wasu kawayensu a gabas ta tsakiya suna kokarin ganin cewa wannan “yerjejeniyar” ta tabbata, amma alhamdullah abinda muka gani ya zuwa yanzun, wannan yerjejenioyar ba zata kai labari ba.

Ba don kome ba, sai don tana nufin kwace hakkin Palasdinawa da musulmin a yankin ne gaba daya, kuma zamu ci gaba da yakarta har zuwa faduwarta.

Da ya koma kan HKI kuma sayyid Nasarrall ya kara jaddada cewa kungiyarsa tana da isassun makamai masu linzami wadanda zata tunkari HKI da su a duk lokacinda ta yi wawta da cilla makami kan kasar Lebanon.

Nasarralla ya ce kungiyar tana da isassun makamai masu linzami, ba don tana da masana’artar makaman a cikin kasar Lebanon ba, amma ko shi dimma idan tana so tana iya samar da shi a cikin kasar.

Daga karshe sayyeed Nasarral ya ce, kungiyoyi masu gwagwarmaya a cikin kasar Palasdinu ma, suna da makamai masu linzami da zasu iya cillawa kan birnin Telabib da wasu wurare a duk lokacinda HKI ta yi tunanin bude yaki da su.

Nasarrallah ya kara da cewa, a duk lokacinda HKI ta fara yaki da kungiyar Hizbullah, kungiyar zata yi amfani da wadanann makamai kan dukkan wurare da suke kasar Palasdinu da aka mamaye. Kuma da haka zata sauya yanayin gabas ta tsakiya gaba dayansa.

Har’ila yau Sayyed Nasarral ya bayyana gazawar kasar Saudiya a gaban jiragen yakin marasa matuka na mutanen kasar Yemen, don ta kasa kare kanta daga hare-haren da mujahidin kasar suke kaiwa kan cibiyoyin man fetur na kasar.

Da wannan dalilin ne, ta rude ta kuma kira kasashen musulmi da kuma na larabawan yankin tekun farisa don samun goyon bayansu.

 

3816148

 

captcha