IQNA

Sojoji Sun Kashe Masu Zanga-Zanga A Sudan

23:06 - June 03, 2019
Lambar Labari: 3483705
Sojojin kasar Sudan sun afkawa masu gudanar da zaman dirshanagaban ma’aikatar tsaron kasar a birnin Khartumasafiyar yau, inda suka kashe mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Mai aiko ma tashar alalam raotanni daga birnin Khartum ya bayar da rahoton cewa, sojojin sun kaddamar da farmakin ne

A safiyar yau, inda suka bude wuta kan jama’a, tare da kashe mutane 15, yayin da bangarorin jam’iyyun adawa sun tabbatar da mutuwar mutane 14, wasu fiye da 60 kuam sun samu munanan raunuka.

Jam’iyyun siasa masu adawaa kasar ta Sudan sun kirayi jama’a da su ci gaba da borensu na lumana, kada su bari a ttunzura su domin daukar matakan yin kisan kiyashi a kansu.

Haka nan kuma jam’iyyun styasar sun dora alhakin abin day a faru kan majalisar sojojin kasar wadda ta kwace iko bayan al’umma sun kori Albashir, tare da bayyana a sojojin a matsayin ‘yan koren Albashir da suke daukar fansa a kan mutane bayan kifar da shi.

Al’ummar Sudan na bukatar sojoji su mika mulki ga hannun farar hula, yayin da sojojin suke ta jan kafa kan wannan batu. Majalisar sojin Sudan tana samun goyon baya da dauki ne daga gwamnatocin Saudiyya, da hadaddiyar daular larabawa da kuma Masar.

 

3817082

 

captcha