Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, kwamitin manyan lokitocin kasar Sudan ya bayar da bayanin cewa, ya samu tabbaci kan cewa, an jefa gawawwakin wasu daga cikin masu zaman dirshan da sojoji suka kashe a cikin kogin Nilu.
Bayanin kwamitin ya ce, wasu daga cikin shedun gani da ido sun tabbatar da cewa, bayan da jami'an sojo dauke da muggan makamai suka auka kan masu zaman dirshan din, sun bude wuta a kansu, tare da tarwatsa jama'a.
Daga nan nan kuma sojojin sun dauke wasu daga cikin gawawakin mutanen da suka mutu, inda aka samu bayanin cewa sun jefa su cikin tekun Nilu.
Kwamitin ya ce akwai kamshin gaskiya a cikin wannan magana, domin kuwa an tsamo wasu daga cikin gawwakin ne a cikin ruwan Nilu.
Akalla mutane talatin da biyar ne dai aka tabbar da mutuwarsu bayan farmakin da sojojin na Sudan kai kan masu zaman dirshan a gabanginin ma'aikatar tsaroa birnin Khartum.