IQNA

23:56 - June 13, 2019
Lambar Labari: 3483734
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa akwai shakku matuka dangane da harin da aka kai yau a kan jiragen dakon mai a tekun Oman.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, akwai shakku matuka dangane da harin da aka kai yau a kan  jiragen dakon mai a tekun Oman da kuma manufar yin hakan.

Ya ce an kai wadannan hae-hare ne a daidai lokacin da frayi ministan Japan yake ganawa da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran, wanda kuma manufar ziyarar asa ita c yadda za a samar da hanyoyin zaman lafiya a yankin.

 

3819138

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: