IQNA

23:53 - June 14, 2019
Lambar Labari: 3483736
Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya zargi Amurka da cewa ita ce babban hadaria yanzu ga zaman lafiyar duniya, tare da hankoron tilasta duniya baki daya bin manufofinta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jamhuriya musulinci ta Iran, ta yi watsi da zargin Amurka, na cewa Iran din ce keda hannu a hare haren da da aka kai wa wasu jiragen ruwan dakon man fetur a teku a jiya Alhamis.

Shugaban kasar Iran Dakta Hassan Rohani, ya zargi Amurka, da zama babbar barazana ga zaman lafiya a yankin da kuma duniya baki daya.

Rauhani ya bayyana hakan ne a zaman taron shugabannin kasashe mambobi na kungiyar Shanghai, inda wanda ke gudana a birnin Bishkek na Kasar Kyrgystan.

Ya ci gaba da cewa, ko shakka babu abin da kasar Amurka take yi a halin yanzu na yin hawan kawara kan dokoki da kaidoji da kuma yin fatali da yarjeniyoyi na kasa da kasa, na a matsayin babbar barazana ga duniya baki daya.

Haka nan kuma ya yi siahara da wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin kasashen Asia domin tunkarar irin wannan barazana, matukar dai kasashen nahiyar suna son su ci gaba da rayuwa cikin ‘yan da daukaka tare da al’ummominsu.

Kafin hakan dama, ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya maida martini kan zargin na Amurka, inda ya ce, babu kamshin gaskia ko kadan a zargin da Amurka ke wa kasarsa na kai hari kan tankokin man guda biyu a jiya, inda a cewarsa Amurka na neman dagula al’amuran da ake ciki ne kawai a yankin.

Ministan ya bayyana hakan a shafinsa inda ya ce wannan harin makircin siyasa ne wanda aka shirya aiwatar da shi a daidai lokacin da Abe ke ziyara a Iran domin sasanta rikicin Amurka da Iran.

Amurka dai ta bakin sakataren harkokin wajenta, ta ce an samu tabbacin wasu hotunan bidiyo da ke nuna dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran na cire wasu abubuwa da Amurkar ta ce nakiyoyi ne da ba su fashe ba daga cikin daya daga jiragen ruwan.

Tuni dai kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi taron gaggawa kan batun, saidai an samu sabanin ra’ayi tsakanin kasashen mambobin kwamitin, inda wasu ke cewa kamta a yi bincike ne kafin daukar duk wani mataki a kan batun.

To sai wasu masana kan harkokin tsaro sun yi zargin cewa hadaddiyar daular larabawa ita ce abin tuhuma kan wannan lamari, domin akwai wasu alamu da suke nuna cewa tana hannu a cikin lamarin, da nufin wargaza duk wani yunkurin sasanta Amurka da Iran.

3819205

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rauhani ، shanghai ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: