IQNA

23:01 - June 16, 2019
Lambar Labari: 3483744
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Sudan na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon farmakin sojoji a cikin 'yan kwanakin nan ya haura zuwa 128.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kwamitin likitocin kasar Sudan ya sanar da cewa, sakamakon farmakin da sojoji suka kaddamar kan fararen hula masu zaman dirshan a cikin birnin Khartum karshen watan ramadan, adadin wadanda suka mutu ya kara haurawa zuwa 128.

Bayanin ya ce adadin ya karu ne sakamakon munanan raunuka da daruwan mutane suka samu sakamakon harin, wanada sojojin suka kashe mutane da harsasai masu rai, kamar yadda kuam aka kara samo wasu gawawwakin da aka jefa a cikin koramar nilu.

Wannan hari da sojojin suka kaddamar kan fararen hula masu adawa da mulkin soji ya fuskanci akkakusar suka da Allawadai daga ko'ina cikin fadin duniya, yayin da kuma kungiyar tarayyar Afrika ta kori Sudan daga cikin ammbobin kungiyar har zuwa lokacin da za a mika mulki ga hannun farar hula.

Sojojin da suke rike da ragamar mulkia  Sudan, sun ki amincewa a gudanar da bincike kan wannan ta'asa, kamar yadda kuma suka ki amincewa da shawarwarin da aka gabatar domin warware matsalar.

3819824

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: