IQNA

23:55 - June 21, 2019
Lambar Labari: 3483760
Bangaren kasa da kasa, dubban Falasinawa ne suka gudanar da gangamia cikin sansanonin su da ke kasashe makwabta domin nuna rashin aminewa da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillanicin labaran iqna ya habarta cewa, dubban daruruwan falastinawa a yau sun nuna fushinsu kan shirin da Amurka take da shi tare da wasu kasashen larabawa na gudanar da abin da suke kira yarjejeniyar karni.

Falastinawa da suke a sansanoninsua  cikin kasashen Syria, Lebanon da kuma Jordan, sun gangami tare da bayyana fushinsu, inda suka bayyana larabawan da suke shirin halartar taron Manama da cewa maha’inta ne.

Amurka tare da haramtacciyar kasar Isra’ila gami da wasu kasashe larabawa da suka hada da Saudiyya, Masar da kuma hadaddiyar daular larabawa ne suka shirya abin da ake kira da yarjejeniyar karni.

Falastinawa na kallon wannan shiri a matsayin wani sabon salon yaudara, da kuma neman mayar da su karkashin danniyar Isra’ila a hukumance, lamarin da suka ce ba za su taba mincewa da shi ba.

 

3821103

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: