IQNA

PLO Ta Fitar Da Bayani Dangane Da Zaman Taron Bahrain

14:56 - June 27, 2019
Lambar Labari: 3483778
Kungiyar gamayyar kungiyoyin kwatar ‘yancin falastinawa ta PLO ta fitar da bayani da ke bayyana matsayinta kan taron birnin Manama na Bahrain a kan Palestine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kungiyar PLO ta fitar da bayani da ke nuna rashin amincewarta da zaman taron Bahrain, wanda ta bayyana shi da cewa ba ya wakiltar al’ummar Palestine.

A cikin bayanin nata, PLO ta bayyana cewa, babban abin da al’ummar PFalastinu ke bukata shi ne adalci a kan lamarinsu, yayin da zaman taron manufarsa ita ce tabbatar da zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Palestine, akan haka ba za su taba amincewa da duk wani abin da taron zai cimamwa ba.

Tun kafin wannan lokacin dai shugaban falastinawa Mahmud Abbas Abu mazin ya sanar da cewa ba za su halarci taron na Bahrain ba, bayan da aka aike masa da goron gayyata.

Babbar manufar taron na Bahrain dai kamar yadda masu shirya shi suka ambata shi ne samar da hanyoyi na saka hannayen jari a  cikin yankunan falastinawa, amma a karkashin iko da kuma kulawar Isra’ila.

3822748

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha