IQNA

23:58 - June 27, 2019
Lambar Labari: 3483779
Bangaren kasa da kasa, kungiyar mata musulmi masu kare hakkokin bil adama ta fara gudanar da zaman taronta na shekara-shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kungiyar mata lauyoyi musulmi “Karama” ta kasar Amurka , ta fara gudanar da zaman taronta na shekara-shekara tare da halartar wakilan wasu daga cikin kungiyoyin musulmi da ma wasu masu rajin kae hakkokin dan adam a ciki da wajen kasar.

A zaman taron wanda zai dauki tsawon makonni uku ana gudanar da shi, ana tattauna batutuwa da suka shafi yanayin hakkokin musulmi da kuma yadda ake samun karuwar nuna kyama  a gare su a cikin Amurka da wasu kasashen yammacin turai.

Taron na da nufin kara wa juna sani kan muhimamn abubuwan da ya kamata kungiyar ta mata lauyoyi musulmi ta mayar da hankalia  akansu wajen kare hakkokin musulmi a Amurka, musamman ma mata musulmi wadanda su ne aka fi cutarwa.

Akwai wakilai mata lauyoyi musulmi da suke halartar taron daga kasashen ketare, da suka hada da Iraki, Syria, Najeriya, Kenya, Faransa, saudiyya da kuma Pakistan.

Baya ga haka kuma akwai wakilan kungiyoyin musulmi daga wasu jihohin kasar ta Amurka, kuma ana gudar da taron ne a halin yanzu a garin West Oak Lane da ke cikin jihar Philadelphia.

 

3822669

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: