IQNA

14:43 - June 28, 2019
Lambar Labari: 3483782
Bangaren kasa da kasa, A daren sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi bafalatine har lahira a unguwar Al-isawiyyah da ke gabashin birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a  daren jiya sojojin yahudawa sun kai farmaki kan wasu matasa da suka taru a unguwar Alisawiyya da ke gabashin Quds domin nuna rashin amincewarsu da makircin da wasu kasashen larabawa suke kitsawa al’ummar Palestine.

Sojojin yahudawan sun bude wuta a kan matasan, inda harsashin bindiga ya samu Muhammad Samir Ubaid, wani matashi dan shekaru 20 da haihuwa, wanda bai jima da fitowa daga gidan kason yahudawan ba, a nan take ya yi shahada, wasu kuma suka samu raunuka.

Tun bayan faruwar lamarina  daren jiya, sojojin yahudawan sun kafa shigaye da kuma hana shiga da fita  a unguwar.

                                                                                            

3822927

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: