IQNA

Larijani: Iran Ta Saba Yin Tsayin Daka A Gaban Makiya

22:53 - July 02, 2019
Lambar Labari: 3483799
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa a tsawon tarihi al'ummar kasar Iran sun jajirce da kuma tsayin daka wajen kalubalantar makiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yayin da yake gudanar da jawabi a taron tunawa da kuma girmama Iraniyawan da suke yi shahada sakamakon harbo jirgin fasinjan kasar Iran da jirgin ruwan yakin kasar Amurka ya yi, Shugaban Majalisar dokokin kasar Iran Dakta Ali Larijani ya yi ishara kan irin ta'addancin da Amurka ta aiwatar kan al'ummar Iran.

Ya ce Al'ummar kasar Iran ba za ta manta da irin ta'addancin da hukumomin kasar Amurka suka aiwatar kan su cikin Tahiri ba, kama  daga juyin milki na ranar 18 ga watan Murdad wanda ya yi daidai da watan Augustan shekarar 1953 M, da kuma umarnin da suka bawa tsohon shugaban kasar Iraki saddam Hussieni na kawo wa kasar hari , da kuma halbo jiragen fajinsan kasar a Tekun Fasha.

Yayin da yake ishara kan takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar ta Iran, Larijani ya ce Amurkawa suna tunanin cewa takunkumi da barazana zai sanya al'ummar kasar Iran su mika wuya, kuma zai iya tayar da yamutsi a cikin kasar Iran, to shakka babu sun yi kuskure a lissafinsu.

Shugaban Majalisar dokokin kasar Iran ya kara da cewa matsalar Amurka a yankin yammacin Asiya shi ne rashin fahimtar al'adun iran sannan suna tunanin cewa idan suka aiko  da babban jirgin yakinsu zuwa yankin, Iran za ta mika wuya.

Larijani ya ce duk da irin kokarin da Amurka ke yi na kafa kawance na kalubalantar kasar Iran bai ci nasara ba.

A wannan Talata ce aka gudanar da taron tunawa da kuma girmama shahidai da kasar Amurka ta kashe a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 1988 bayan ta harbo jirgin fasinjan kasar Iran da suke ciki wanda ya tashi daga birnin Bandar Abbas kan hanyarsa zuwa birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa.

A yayin kai wannan hari dukkanin fasinjan dari biyu da casain da kuma ma'aikatan jirgin sun yi shahada, daga cikinsu kuma akwai kananen yara satin da shida da Mata 53 da kuma 'yan kasashen waje arbain da shida.

3823801

 

 

captcha