IQNA

Martanin Kungiyar kasashen Larabawa Kan Yunkurin Rusa Masallacin Aqsa

22:55 - July 02, 2019
Lambar Labari: 3483800
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen larabawa ta mayar da martani dangane da yunkurin Isra’ila na rusa masallacin quds.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kungiyar kasashen larabawa ta fitar da wani bayani wanda a cikinsa take yin Allawadai da yunrin Isra’ila na rusa masallacin aqsa ta hanyar tona ramie  karkashinsa.

Bayanin ya ce wanann matakin da Isra’ila take dauka na tsokana newanda kuma dukkanin larabawa da msuulmi ba za su taba amincewa da shi ba.

Kungiyar kasashen larabawa ta kirayi Isra’ila da ta gaggauta dakatar da gina ramuka a karkashin ginin masalalcin Aqsa, tare da yin kira ga dukkanin kasashen duniya das u takawa Isra’ila burki kan wannan yunkuri.

Tun kafin wannan lokacin dai Falastinawa sun sha kokawa kana bin da Isra’ila take na tona manyan ramuka a karkashin masalalcin quds, wanda hakan zai iya sanya masalalcin ya rufta  akowane lokaci, amma babu wata asa daga cikin kasashen larabawa da t ace uffan kan batun.

3823647

 

 

 

 

 

captcha