IQNA

OIC Ta Yi Gargadi Kan Karuwar Kyamar Musulmi A Sri Lanka

23:59 - July 04, 2019
Lambar Labari: 3483807
Bangaren kasa da kasa, kungiyar OIC ta yi gargadi kan karuwar kyamar musulmi a kasar Sri Lanka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar kasashen musulmi ta bayyana karuwar kin jinin musulmi a kasar Sri lanka da cewa lamari ne mai matukar daga hankali.

Bayanin kungiyar ya ce musulmi su ne marassa rnjayea  kasar ta Sri Lanka kan haka kare hakkokinsu da rayukansu da dukiyoyisu abu ne da ya rataya kan mahukuntan kasar.

Tun bayan harin da kungiyar yan ta’adda ta daesh ta kaia  kasar Sri Lanka a ranar 21 ga watan Afirilun da ya gabata, tare da kashe mutane 50 ad jikkatawa wasu kimanin 500, kyamar musulmi ta karu a kasar.

Kasha 9.2 na al’ummar Sri Lanka musulmi ne, ayyin da yan adinin buda su n suka fi yawa a kasar, sai kuma addinin hindu da kuma kiristoci.

3824487

 

 

captcha