IQNA

23:49 - July 06, 2019
Lambar Labari: 3483810
Sojojin dake rike da mulki da wakilan masu bore a Sudan, sun cimma matsaya ta kafa wata hukuma da zata jagoranci gwamnatin wucin wucin gadi da za’a kafa nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Da yake samar da hakan yayin wani taron manema labarai, mai shiga tsakani na kungiyar tarayya Afrika, ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya ce ta kafa hukumar da zata jagoranci gwamnatin rikon kwarya ta tsawan shekaru uku.

Za’a kafa hukuma ce mai cin gashin Kanata, wacce kuma zata kasance da karba karba ce tsakanin sojojin da fararen hula, ta kimanin tsawon shekaru hudu ko fiye a cewar jami’in, saidai ba tare da fayyace tsarin da za’a kafa wannan hukuma ba.

Amma a cewarsa da farko sojoji ne zasu jagoranci hukumar na tsawon watanni 18, kafin wani farar hula ya karba har zuwa karshen rikon kwarya.

Ana ganin wannan a matsayin wata alama ta kawo karshen rikicin kasar, tun bayan kifar da mulkin shugaba Umar Hassan Al-bashir.

A ranar Laraba data gabata ne bangarorin dake rikici a Sudan, suka koma kan teburin tattaunawa, bayan da katse tattaunawar ta tsakaninsu biyo bayan da sojoji sukayi amfani da karfi wajen murkushe masu zaman dirshin a ranar 3 ga watan Yuni da ya gabata a gaban hedikwatar sojin kasar.

3824705

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: