IQNA

23:43 - July 08, 2019
Lambar Labari: 3483818
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin jihar Cuebec a Canada ta kafa sharadin cire hijabi a kan Malala Yusufzay.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na Anatoli cewa, Jean Francois Robber kwamishinan ilimi na jihar Cuebec  kasar Canada cewa, dole ne Malala Yusuf Zay ta cire hijabi idan har za ta koyar a jihar.

Wanann na zuwa  ne bayan kafa dokar da gwamnatin Jihar ta Cuebec ta yi ne, kan cewa dole ne malaman makarantu su cire duk wata sutura da addini a lokacin da suke cikin aiki.

A lokacin da wani dan jarida ya tambaye Robber ko Malala Yusufzay za ta koyarwa a cikin makarantun Cuebec, sai ya amsa da cewa za ta iya yin hakan, amma bisa sharadin cewa sai ta cire lullubi daga kanta.

Wannan mataki dai yana shan suka daga kungiyoyin kare hakkokin mabiya addinai a kasar ta Canada, da kuma kungiyoyin kare hakkokin bil adama da dama a cikin kasashen duniya.

Wannan dokar dai za ta fi shafar mata musulmi ne wadanda suke saka lullubi a kansu, inda hakan yake a matsayin wani sabon mataki na takura rayuwarsu a kasar.

 

3825304

  

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Malala ، Canada ، hijabi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: