IQNA

23:53 - July 09, 2019
Lambar Labari: 3483822
Gamayyar kungiyoyin kwadgo ta kasar Tunisia ta gudanar da wani babban jerin gwanoa birnin Tunis, domin tir da Allawadai da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya dubban jama’a ne suka taroa  birnin Tunis domin yin tir da Allawadai da shirin nan na yarjejeniyar karni, wanda Amurka da Isra’ila da wasu kasashen larabawa suka shirya, da nufin tabbatar da sanuwar Isra’ila a cikin Palastinu.

Masu gangamin sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga al’ummar Palastine, da kuma yin Allawadai da sarakunan larabawa da suka mika kai ga manufofin Amurka da Isra’ila, domin sayar da Palastine da al’ummarta.

Nawaluddin Al-Tubi babban sakataren gamayyar kungiyoyin kwadago a kasar Tunisia ya bayyana a wajen gangamin cewa, batun falastinu shi ne na farko kuma mafi muhimmanci a wurin dukkanin al’ummar Tunisia, da ma larabawa da musulmi baki daya.

Inda ya jaddada cewa ba za su taba mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin mallaka ba, ko da kuwa wasu daga cikin shugabannin larabawa sun mika kai bori ya hau.

 

3825557

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: