IQNA

22:54 - July 13, 2019
Lambar Labari: 3483836
bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kakkausar suka kan 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka musulmi Ilhan Umar da kuma Rashida Tlaib.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Independent ta bga wani rahoto da e cewa, Donald ya sake yin kalamansa na suka kan ‘yan majalisar dokokin Amurka musulmi su biyu, da kuma shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi.

A cikin kalamansa Trump ya bayyana abin da wasu daga cikin masu aidarsa ta kin musulmi da kuma bakia  kasar Amurka da cewa, kalamai ne na kin ‘yan majalisar biyu wadanda musulmi ne da kuma shugabar majalisar da suke jam’iyya daya da ita.

Wasu daga cikin masu tsananin kiyaya da musulmi suna yin suka a kan shafukan yanar gizo a kan ‘yan majalisar musulmi, inda Trump ya nuna jin dadinsa kan hakan.

Kafin wannan lokacin dai Trump ya bayyana cewa ya kamata a kori Ilhan Omar da take shiga majalisar dokokin Amurka da lullubi na addinin musluncia  kanta.

Ilhan Omar dai ‘yar asalin kasar Somalia cewa, zuwa Amurka kuma ta lashe zaben ‘yar majalisa a 2018, bayan da ta shiga Amurka a cikin shekara ta 1992 a matsayin ‘yar gudun hijira.

3826772

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: