IQNA

23:47 - July 15, 2019
Lambar Labari: 3483842
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron girmama mahardata kur’ani mai tarki su 225 a kasar Tunsia.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar KUNA na kasar Kuwait cewa, a  jiya an girmama mahardata kur’ani mai tarki su 225 a kasar Tunsia a wani shiri da aka shirya musu.

Manufar shirin dai ita ce girmama wadannan mutane da suka nuna kwazo wajen hardar kur’ani mai tsarki, wanda kuma wannan bas hi ne karon farko da ake gudanar da shi ba.

A wurin taron girmama mahardatan, an samu halartar malamai da kuma jami’an gwamnati, musamman daga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

A lokacin da yake halartar wurin, jakadan kasar Kuwait a kasar Tunisia, ya bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin mahardatan su 225 , tare da yin alkawalin Dakar nauyinsu wajen ci gaba da karatukansu.

Kasar Tunisia dai na daga cikin kasashe da suke mayar da ankali matuka ga harkar kur’ani mai tsarki.

 

 

3827206

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: