IQNA

Taron Kusanto Da fahimta Tsakanin Kiristoci Da Musulmi

23:52 - July 15, 2019
Lambar Labari: 3483844
Bangaren kasa da kasa, mabiya mazhabar shi’a a kasar afrika ta kudu sun shirya taro da ya hada musulmi da kiristoci.

Hojjatol Islam Sayyid Hussaini daya daga cikin malaman mabiya mazhabar shi’a  akasar Afrika ta kudu ya jagoranci shirya taro shirya taro da ya hada musulmi da kiristoci domin kara samun fahimtar juna da kuma zaman laiya.

A lokacin gudanar da zaman taron, an samu halartar bangarori daban-daban na musulmi da suka hada da ‘yan sunna da ‘yan shi’a da kuma wasu bangarori na muuslmi, kamar yadda kuma kiristoci daga bangarori daban-daban su ma suka halarci taron.

Dukkanin bangarorin biyu sun gabatar da jawabai na kara karfafa fahimtar juna da girmama juna da kuma yin aiki tare a bangarori na ‘yan adamtaka da karfafa zaman lafiya da taimakon mutanea  dukkanin bangarori na rayuwa.

Wannan shi ne abin da dukkanin addinai  da aka saukar daga sama suke koyar da mabiyansu, wanda kuma shi ne dabiun dukkanin annabawan Allah.



3827314

 

 

captcha