IQNA

23:56 - July 18, 2019
1
Lambar Labari: 3483854
Bangaren kasa da kasa, kotun Kaduna ta sake dage sauraren shari'ar sheikh Ibrahim Zakzaky da aka gudanar a yau a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau ne kotu da ke sauraren shari’ar Sheikh Zakzaky a Kaduna ta sake gudanar da zamanta, inda kuma ta dage sauaren shari’ar zuwa karshen wannan wata na Yuli.

Rahotanni daga jihar Kadua sun Ambato cewa, a yau an gabatar da Sheikh Zakzaky agaban kotun da ke sauraren shari’arsa, inda aka sa ran kotun za ta yi dubi kan rahoton da aka gabatar mata dangane da batun rashin lafiyarsa.

Alkalin kotun ya sanar da cewa an dage sauraren shari’ar zuwa karshen wannan wata, domin samun damar yin dubi a kan rahoton da aka gabatarwa kotun kan batun rashin lafiyar Shikh Zakzaky, wanda rahoto ne da likitocin da suka bincika lafiyarsa ne suka gabatar.

A cikin rahoton likitocin sun bayyana sakamakon gwaje-gwajen da aka gudanar bayan daukar jininsa a watannin baya, wanda ya nuna cewa yana fama da matsaloli masu yawa, daga ciki har da samun guba a cikin jininsa.

Likitocin sun bukaci da a bayar da damar fitar da shi domin duba lafiyarsa, kamar yadda lauyoyi masu kare shi suka gabatar da wannan rahoto a cikin korafe-korafen da suka gabatarwa kotun.

Kotun dai za ta koma zamanta nearanar 29 ga wannan wata na Yuli kamar yadda alkalin kotun ya sanar.

 

3828137

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zakzaky ، Najeriya ، Kaduna
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
INUWA MUHD
0
0
allah yana bayan megaskiya in sha allahu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: