IQNA

23:52 - July 20, 2019
Lambar Labari: 3483860
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Amurka ta yabawa gwamnatin kasar Argentina kan saka kungiyar Hizbullaha cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayar da rahoton, Amurka ta jinjina wa gwamnatin Argentina, dangane das aka kungiyar Hizbu;aha  cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Bayanin ya ce a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Argentina Mauricio Macri a ziyarar da yake kaiwa a kasar, Mike Pompeo sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya isar da godiyar gwamnatin Amurka ga shugaban na Argentina kan daukar wannan mataki.

Haka nan kuma bayanin ya ce baya ga tattauna batutuwa na kyautata alaka tsakanin Argentina da Amurka, bangarorin biyu sun tattauna kan batun yin aiki tare wajen yaki da ta’addanci.

Gwamnatin kasar Argentina mai ci yanzu wadda take yin biyayya sau da kafa ga Amurka, na hankoron ganin ta farantawa Amurka ta hanyar saka kungiyar Hizbulla a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kafin ziyarar ta Pompeo, Isra’ila da wasu daga cikin jami’an gwamnatin Trump sun aike da sakon godiya ga shugaban na kasar Argentina kan wannan mataki, kamar yadda kuma kasar ta Argentina take da niyyar rufe wasu asusun ajiya  awasu bankuna na kasar da take zaton cewa suna da alaka da Hizbullah.

 

3828489

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Argentina ، Amurka ، hizbullah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: