IQNA

23:53 - July 22, 2019
Lambar Labari: 3483869
Bangaren kasa da kasa, an fara gyaran wani kwafin kur'ani mai tsarki mai shekaru 455 a kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillacinTurk press ya bayar da rahoon cewa, Ahmad Qurnaz wani kwararre kan gyaran kayan tarihi yana gudanar ad aikin gyaran dadaden kur’ani a Turkiya.

Bisa ga dalilai na tarihi da aka dogara da su, kur’ani yana da kimanin shekar 455 a halin yanzu da rubutawa, wanda wata mata Disaz matar sarki Mahmud na biyu an Daular Usmaniyya ta bayar da shi kyauta ga gidanan sarautar daular a watan Yulin 1816.

Wani mutum mai suna Ali da aka fi sani da Abul Hassan Alasili shi ne ya rubuta kur’anin, wanda ya kammala a ranar 10 ga watan Fabrairu 1564.

Qurnaz ya cea  kowace rana yana ware sa’oi 5 zuwa 6 ga wanan aiki na gyaran wannan kwafin kur’ani.

Ya ce tun watanni 6 da suka gabata ya fara aikin, kuma yanzu yana cikin mataki na karshe, kuma da zaran ya kammala, za a mika kur’ani ga bababn dakin ajiye kayan tarihi na kasar Turkiya.

 

 

3828979

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: