IQNA

23:19 - August 12, 2019
Lambar Labari: 3483939
Bangaren kasa da kasa, sheikh Ibrahim Zakzaky zai fita zuwa kasashen ketare domin neman magani.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau ne ake sa ran Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harkar Musulunci a Najeriya zai bar kasar zuwa kasar India domin neman magani, bisa rashin lafiyar da yake fama da ita.

Rahotannin sun tabbatar da cewa Sheikh Zakzaky da wadanda suke tare da shi za su kama hanya a yau zuwa kasar India domin neman magani kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

A zaman da kotun ta gudanar a ranar Litinin da ta gabat ce alkalin kotun da ke sauraren shari'ar Sheikh Zakzaky, ya bayar da dama gare shi tare da mai dakinsa domin su fita zuwa kasar India domin neman maganai, bayan da alkalin ya yi nazari kan sakamakon bincike da likitoci suka fitar kan yanayin rashin lafiyarsa da mai dakinsa, wanda lauyoyin sheikh Zakzaky suka mika masa.

Daya daga cikin lauyoyin sheikh Zakzaky ya sheda wa tashar Hausa VOH cewa, Sheikh Zakzaky ne da kansa ya bukaci zuwa kasar at India, kamar yadda kuma shi ne zai dauki nauyin dukkanin ayyukan da za a yi na jinyarsa.

 

3834406

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ketare ، sheikh zakzaky ، India
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: