IQNA

23:21 - August 12, 2019
Lambar Labari: 3483940
Bangaren kasa da kasa, falastinawa fiye da dubu 100 ne suka yi sallar Idin babbar salla  a cikin masallacin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Almayadeen ta bayar rahoton cewa, duk da irin tsauraran matakan da jami’an tsaron yahudawa suka dauka dubban falastinawa ne suka halarci sallar idi a jiya a cikin masallacin aqsa.

Bisa abin da ya zo cikin wannan rahoto, falastinawa fiye da dubu 100 ne suka halarci wannan sallar idi, inda suka fito domin kare masallacin quds da ke keta alfarmarsa da yahudawa suke yi.

A daidai lokacin da ake gudanar da sallar idi, wasu gungun yahudawan sahyuniya sun yi gangami da nufin tsokanar falastinawa a wurin, inda daga bisani tare da taimakon jami’an tasron Isra’ila, yahudawan suka afka kai cikin masallacin.

3834166

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Quds ، aqsa ، masallacin ، falastinawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: