IQNA

23:43 - August 17, 2019
Lambar Labari: 3483957
Bangaren kasa da kasa, bayan dawowarsa daga kasar India jami’an tsaro sun wuce tare da sheikh Zakzaky daga filin jirgin Abuja.

Kamfanin dillancin labaran iqna, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada bayanai dangane da dalilan da suka sa ta dawo da sheikh Ibrahim El-Zakzagi da matarsa gida daga kasar Indiya kwanaki kadan da zuwansu kasar don jinya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ya nakalto babban sakatari a ma’aikatar watsa labarai da kuma al-adu na Najeriya Grace Gekpe tana fadar dalilan, wadanda suka hada da cewa Sheikh Ibrahim Elzakzaki ne ya zabi asbitin da aka kaishi a birnin New Delhi da kansa, tun kafin a yi tafiyar, amma da ya isa can sai ya fara haduwa da wasu lawyoyi don neman mafakar siyasa a kasar.

Mrs Grace Gekpe ta ce shugaba harka Islamiya a Nigeriyaya hadu da wakilan wasu kungiyoyi masu zamna kansu wadanda suka hada da Islamic Human Rights Commission da wasu kungiyoyin yan shi’a don cimma manufofinsa.

Amma a wani jawabin da da aka yada a shafuskan sadarwa Sheikh Ibrahim Elzazaky ya nuna damuwarsa da irin yadda jama’an tsaron Najeriya da na kasar Indiya suka takura masa a asbitin da aka kai shi sannan sun hana shi haduwa da likitocin da ya amince da su.

Har’ila yau Ibrahim Musa shugaban dandalin yada labarai na IMN ya bayyanwa yan jaridu cewa Sheikh Zakzaki ya zabi dawowa gida ne bayan da ya sami sabani da asbitin da aka kai shi jinya, kan likitocin da zasu duba lafiyarsa da kuma yadda za’a yi masu jinya.

A halin yanzu dai jam’an tsaron Najeriya, wadanda ake zaton na hukumar DSS ne sun tafi da shi jim kadan bayan isarsa gida Najriya a jiya jumma’a.

3835610

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: