IQNA

23:48 - August 17, 2019
Lambar Labari: 3483958
Bangaren kasa da kasa, a yau ake rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu tsakanin sojoji da ‘yan siyasa a Sudan kan kafa gwamnatin rikon kwarya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wannan Asabar ce al’ummar Sudan ke gudanar da bikin kafa tarihi na sanya hannu kan yarjejeniyar karshe na kundin tsarin mulki da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Bikin na wannan Asabar shi ne babban buki da al’ummar kasar za su gudanar tun bayar faduwartsohuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir a ranar 11 ga watan Afirilun wannan shekara.

Sabuwar yarjejeniyar ta kunshi wa’adin mulkin gwamnatin rikon gwarya tsakanin Majalisar Sojoin kasar da gamayyar kungiyoyin neman ‘yanci da jam’iyyun siyasa na tsawon watanni 39.

Gwamnatin rikon gwaryar dai za ta kunshi Mutane 11, biyar daga bangaren Majalisar Sojin kasar da kuma biyar daga bangaren gamayyar kungiyoyin gwagwarmayar neman ‘yanci da sauyi, mutum guda kuwa wanda zai samu amincewar dukkanin bangarorin biyu.

Bikin na yau dai yana samun halartar manyan baki daga kasashen Duniya ciki kuwa har da ministan harakokin wajen kasar Turkiya Mevlüt Çavuşoğlu.

Majalisar mulkin sojin sudan din ta dauki kwararan matakan tsaro domin ganin an gudanar da wannan taro lami lafiya.

 

3835440

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: