IQNA

23:50 - August 17, 2019
Lambar Labari: 3483959
Bangaren kasa da kasa, dakarun kasar Yemen sun mayar da munanan hare-hare da jirage marassa matuki a kan babban kamfanin man fetur na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin din al-masirah ta bayar da labarin cewa; An kai harin ne a matsayin mayar da martani dangane da hare-haren wuce gona da iri na bayan nan da kawancen yaki na Saudiyya su ka kai a cikin Yemen

Hare-haren na yau an kai su neda jirage marasa matuki akan cibiyoyin man fetur da su ka hada da kamfanin tace man fetur na al-shaibah na Aramco.

Mai Magana da yawun sojojin Yemen Janar yahya Sari’i, ne ya bayyana cewa: An kai hare-haren da jirage marasa matuki guda 10, sun kuma nufi kamfanin tace man fetur na al-shaibah.”

A cikin kamfanin tace man fetur din na al-shaibah, da akwai rumbun adana fiye da ganagar man fetur biliya daya.

Kakakin sojan kasar ta Yemen ya kuma yi kira ga fararen hula da su kaucewa zama a kusa da cibiyoyi masu muhimmanci na saudiyya domin za a iya kai musu hari a kowane lokaci

Yakin da Saudiyya ta shelanta akan kasar Yemen ya shiga cikin shekara ta biyar. Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutane dubu casain ne aka kashe a tsawon lokacin da aka dauka ana yakin.

3835539

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: