IQNA

23:24 - August 18, 2019
Lambar Labari: 3483960

An Kayata Hubbaren Imam Ali (AS) Domin Idin Ghadir

Bangaren kasa da kasa, an kayata hubbaren Imam Ali (AS) domin murnar idin Ghadir.

An Kayata Hubbaren Imam Ali (AS) Domin Idin Ghadir

Kamfanin dillancin labaran iqna, tun a jiya ne aka fara gudanar da ayyukan kayata hubaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf, domin zagayowar lokacin tunawa da idin ghadir, inda aka saka tutoci masu launin kore a koina a ciki da wajen hubbaren.

Ranar 18 ga watan Zulhijjah dai ita ce ranar da manzon Allah ya ayyana Imam Ali (AS) a matsayin magajinsa a  bayansa bisa ingantattun ruwayoyi daga bangarorin sunnah da shi’a, wanda kuma wannan ranar tana masayin ranar da mabiya ahlul bait suke tunawa da ita.

A ranar Ghadir mabiya ahlul bait suna yin farin ciki da abin da ya faru na ayyana jagoran ahlul bait (AS) a matsayin magajin manzon Allah (SAW) a bayansa, wanda rana e ta tarihi a addinin muslunci.

A irin wannan rana masoya ahlul bait (AS) sukan taru a hubbaren Imam Ali (AS) domin gudanar da taruka na tunawa da wannan rana.

3835723

آذین بندی حرم حضرت علی(ع) به مناسبت عید غدیر + عکس
 
captcha