IQNA

23:55 - August 25, 2019
Lambar Labari: 3483987
Bangaren kasa da kasa, dubban ‘yan gudun hijirar Rohingya a kasar Bangaladesh sun bukaci hakkokinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin tashar arab News cewa, Musulmin Rohigya Suna Korafi Kan Halin Da Suke Ciki

Musulmin Rohingya da suke gudun hijira suna kokawa kan irin yanayin da suka samu kansu a cikin a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Musulmi ‘yan gudun hijirar Rohingya a kasar Bangaladesh sun bukaci hakkokinsu da hakan ya hada ba su hakkokinsu na ‘yan kasa a Myanmar kafin su koma.

Rahoton ya ce adadin wadanda suka taru suka yi gangami ya kai kimanin mutane fiye da dubu 3 a cikin wani sansanin da aka tsugunnar da su a cikin kasar Bangaladesh a inda suke gudun hijira.

A kwankin bayan gwamnatin kasar Bangaladesh ta bukaci ‘yan kabilar Rohingya da suke a kasar da su koma kasarsu Myanmar don kashin kansu ga duk mai bukatar hakan, ba tare da wani tilasci ba, amma babu wanda ya amince da hakan.

Tun a  cikin shekara ta 2017 ce sojojin gwamatin Myanmar suka kaddamar da hare-hare a  kan lardin Rakhin wanda ‘yan kabilar Rohingya musulmi suke zaune a cikinsa.

Sojojin na Myanmar sun kashe dubban musulmi da kuma kone gidajensu da makarantunsu da masallatansu, lamarin da ya tilasta dubban dauruwa tserewa zuwa kasar Bangaladesh inda suke gudun hijira a halin yanzu.

 

 

 

 

3837302

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، rohingya ، myanmar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: