IQNA

23:54 - August 28, 2019
Lambar Labari: 3483994
Bangaren kasa da kasa, an gano wani dadaden kur’ani da aka sace a kasar Masar a lokacin da ake shirin fita da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na Al-tahrir cewa, a jiya jami’an tsaron filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira a kasar Masar sun samu nasarar cafke wani dan Najeriya  alokacin da ayke shirin fita da wani kur’ani mai tarihi da aka sace a kasar.

Rahoton ya ce jami’an tsaron filin jirgin sun gane kur’anin ne bayan da suka yi bincike na X-ray a jikar da take dauke da kur’anin, bayan da suka shakku kana bin da jikar take dauke da shi, inda aka samu wanann kur’ani a cikin jikar, a lokacin da mutumin yake nufin tafiya zuwa birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu.

Wannan kura’ni dai yana daga cikin abubuwan tarihi da ake alfahari da  su a kasar Masar, kuma tarihin lokacin rubuta wannan kir’ani yana komawa tun lokacin khalifa Usman.

3838138

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: