IQNA

23:54 - September 01, 2019
Lambar Labari: 3484007
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya jaddada cewa babu makawa dangane da martanin Hizbullah akan harin Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya jaddada cewa; babu makawa dangane da martanin Hizbullah akan hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Lebanon.
Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na farkon watan Muharram a zaman kwanaki goma na Ashura a birnin Beirut, fadar mulkin kasar Lebanon.
Ya ce Netanyahu ya tabbatar wa duniya da cewa su ne suka kaddamar da hare-hare akan Iraki da Syria da kuma Lebanon a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, a kan haka Hizbullah za ta mayar wa Isra’ila da martani kan hare-harenta a Lebanon.
Haka nan kuma dangane da batun wuraren kera makamai masu linzami na musamman, Sayyid Nasrullah ya ce Hizbullah ba ta da irin wadannan wurare acikin Lebanon, amma ta mallaki irin wadannan makamai masu linzami da aka kera su da fasaha ta musamman, wadanda za su iya kai hari a kowace kusurwa ta Isra’ila.
Sayyid Nasrullah ya gargadi Netanyahu da cewa, wadannan hare-hare suna a matsayin jefa rayuwar yahudawan Isra’ila cikin hatsari ne, domin kuwa martanin Hizbullah a kan Isra’ila zai iya shafar kowane sako na yankunan Falastinawa da yahudawa suka mamaye.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai rundunar sojin Isra’ila ta shirya gudanar da wani atisayi, amma saboda tsoron martanin Hizbullah, ala tilas Isra’ila ta janye gudanar da wannan atisayi a arewacin Falastinu da ta mamaye.

 

3838947

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: