IQNA

23:59 - September 01, 2019
Lambar Labari: 3484009
Bangaren kasa da kasa, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kame jagororin Harka Islamiyya a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin kafofin yada labarai daga Najeriya sun bayar da rahoton cewa, babban sufeton ‘yan sanda na kasar ya bayar da umarnin kame jagororin Harka Islamiyya tare da rushe wuraren tarukansu.

Wannan na  zuwa ne bayan wani hukunci da kotu ta yanke na haramta Harka Islamiyya a karkashin jagorancin sheikh Zakzaky bayan da gwamnatin tarayya ta bukaci hakan daga kotu.

Tun a karshen shekara ta 2015 ne dai ake tsare ad sheikh Zakzaky bayan da aka kame shi a lokacin da sojoji suka kai farmaki a gidansa da ke zaria, tare da kashe adadi mai yawan gaske na mabiyansa a lokacin kaddamar da harin.

3838941

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: