IQNA

23:20 - September 04, 2019
Lambar Labari: 3484015
Bangaren kasa da kasa, mutae 8 sun rasa rayukansu a wani harin bam a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran iqna, majiyoyin tsaro a kasar Mali sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 8sakamakon tarwatsewar wasu bama-bama da aka dana a gefen wata babbar hanya da hada cwasu birane a tsakiyar kasar a jiya Talata.

Jami’an tsaron kasar Mali sun sanar a jiya cewa, an kai harin ne a kan babbar hanya da ta hada biranan Duwintza da Hambori da ke tsakiyar kasar, inda a nan take mutane 8 suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata.

Bayanin ya kara da cewa, wadannan hare-hare suna zuwa ne a ci gaba da kai ruwa rana da ake yi tsakanin kungiyoyin da ke da’awar jihadi, da kuma jami’an tsaroadaya bangaren.

Tun kimanin shekaru 7 da suka gabata ne dai kasar Mali take fama da matsaloli na tsaro, bayan da ‘yan bindiga masu da’awar jihadi suka kwace yankuna da dama na arewaci da kuma tsakiyar kasar Mali, lamarin ya jawo shigar dakarun kasashen ketare a kasar, domin tabbatar da tsaro, da kuma dawo da doka da oda a kasar.

3839895

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Mali ، harin bam
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: