IQNA

23:57 - September 07, 2019
Lambar Labari: 3484026
Bangaren siyasa, kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran ya bayyana cewa, matakin da Iran ta dauka na cikin yarjejeniyar nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wani mataki na ci gaba da matsin lamba na dakatar da aiki da wasu daga cikin sharudan da yarjejeniyar da aka cimma da ita a shekara dubu biyu da sha biyar Iran ta fayyace a yau Asabar, bangarorin da matakin data dauka na uku na jingine aiki da wasu daga cikin bangarori da yarjejniyar nukiliyar ta kunsa.

Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai, kakakin hukumar kula a makamashin nukiliya ta kasar, ya ce, matakin da Iran din ta dauka ya shafi sauyi wajen bincike da kuma bunkasa fasahar nukiliya.

Ciki kuwa har da watsa wani nau’in gas mai suna UF6, a cikin bututtan tatse uranium 20, samfarin IR6, wanda kuma wannan wata hanya ce da zata taimakawa Iran din wajen samun tatsatsan sinadarin na uranium.

Kakakin hukumar, Behruz Kamalvandi, ya kuma ce Iran, kawo yanzu Iran, ba tada niyyar hana wa jami’an hukumar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya shiga cibiyoyi da kuma ayyukan nukiliya na kasar.

A ranar Alhamis data gabata ce shugaban kasar Iran, ya sanar da cewa kasar zata shiga mataki na uku na jingine aiki da wasu daga cikin sharuddan da yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita.

Wannan mataki na zuwa ne kuwa saboda yadda kasashen da suka rage a yarjejeniyar bayan ficewar Amurka, suka kasa tabaka komai wajen shafe mata hawaye, sakamakon zafafan takunkuman da Amurkar ke ci gaba da kakaba mata ba kakkautawa.

 

 

3840563

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Kamalwandi ، shirin ، nukiliya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: