IQNA

23:53 - September 10, 2019
Lambar Labari: 3484036
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, kasa Iran ita ce babbar kasa da ke taimaka ma gungugun ‘yan gwagwamaya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana cewa Hizbullah tana kashedi wa manyan kasashen duniya dangane da duk wani kokarin na farwa Jamhuriyar muslunci ta Iran da yaki.

Babban sakataren kungiyar na Hizbullah ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a safiyar yau Talata wanda yayi dai-dai da ranar ashoora goma ga watan Muharram na wannan shekara.

Sayyeed Nasarallah ya kara da cewa duk wani yakin da za’a kaiwa kasar Iran kamar kunna wutar yaki ne a yankin gaba daya.

Nasarallah ya kara da cewa kungiyar ba zata zama yar kallo ba a duk lokacin da aka farwa kasar Iran da yaki.

Daga karshe Sayyeed Nasarallah ya kammala da cewa duk wani yakin da za’a fadawa kasar Iran da shi, zai zama sababin shafe Isra’ila daga doron kasa, sannan zai kawo karshen samuwar sojojin Amurka a yankin gaba daya.

A yau ne aka gudana da tarukan ashura a kasashen duniya daban-daban, domin tunawa da zagayowar ranar shahadar zuriyar manzon Allah a hannun makiya makiya Allah da manzonsa, waki’ar da ake kallonta a matsayin lamari mafi muni da ya faru da zuriyar manzon Allah bayan fakuwarsa.

3841311

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: