IQNA

23:54 - September 18, 2019
Lambar Labari: 3484061
Bangaren kasa da kasa, an bude wata sabuwar cibiyar hardar kur’ani mai tsarki ta makafia jamhuriyar Dagistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Rasha Islam ya bayar da rahoton cewa a jiya ne aka bude bude sabuwar cibiyar ta hardar kur’ani ta makafia  jamhuriyar Dagistan, tare da halartar babban mai bayar da fatawa na jamhuriyar Sheikh Ahmad Afandi.

Sheikh Ahmad Afandi ya yaba da wannan gagarumin aiki na bude cibiyar koyar da hardar kur’ani mai tsarki ga masu larurar gani a yankin, duk da cewa akwai makarantu masu wannan aiki, amma wannan cibiya ta sh abamban da su.

Ya kara da cewa duk da cewa akwai matsaloli na karancin kayan aiki a bangaren koyar da ilmomin kur’ani, amma wannan cibiya ta yi kokari wajen samar da muhimmai daga cikinsu.

Wannan yanki dai yana cikin kasar rasha ne, kuma ana yin amfani da harshen rashanci ne wajen koyar da dukkanin ilmomin addinin muslucnia wannan yanki wanda akasarin mazauansa musulmi ne.

3843166

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Dagistan ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: