IQNA

23:37 - September 20, 2019
Lambar Labari: 3484068
Bangaren kasa da kasa, baban sakataren Hizullah ya ce za su hana shawagin jiragen Isra’ila a Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar alamanar cewa, Sayyid Hassan Nasrullah baban sakataren Hizullah ya jadda cewa, daga yanzu zasu dauki matakan hana shawagin jiragen Isra’ila marassa matuki a cikin kasar  Lebanon.

Sayyid Nasrullah ya ce kakkbo jirgin liken asirin Isra’’ila da Hizbullah ta yi a kwanakin baya ya sanya a halin yanzu Isra’ila tana taka tsantsan, inda har yanzu ba ta sake tura jirginta  acikin Lebanon ba.

Ya ci gaba da cewa, yana yin kira ga kasashen Saudiyya da su dauki darasi dangane da abin da yake faruwa a yankin, su daina tayar da fitina da yake-yakea  cikin kasashen musulmi da na larabawa, su kawo karshen yakin da suka bude da al’ummar Yemen, domin harin da mutanen suka kai ma Saudiyya dsomin tabi ne, idan Saudiyya taci gaba da wannan yaki abin da zai biyo baya zai fi hakan.

Dangane da kokarin da Saudiyya da kuma UAE suke yi na ganin sun ingiza Amurka ta shiga yaki da Iran, saboda suna ganin za su iya sayen shugaban Amurka da kudi domin yin hakan, to sani cewa hakan yana tattare da gagarumin hadari gae su da ma yankin baki daya.

3843434

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: