IQNA

22:50 - September 24, 2019
Lambar Labari: 3484083
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Aljeriya ta bukacin bunkasa ayyukan hadin gwiwa a bangaren kur'ani tare da kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abarta cewa, a wata ziyara da ya kai jiya a ofishin jakadancin Iran a birnin Aljies, ministan kula da harkokin addini a Aljeriya Yusuf Bilmahdi ya bayyana cewa, suna da bukatar ganin sun yi aiki tare da Iran a bangaren ayyukan kur’ani mai tsarki.

Ya ce kasashen Iran da Aljeriya kasashen msuulmi ne masu matukar muhimamnci, kamar yadda Aljeriya take da muhimamnci a Afrika haka kasar Iran take da muhimamnci a yankin gabas ta tsakiya baki daya, saboda hakan yin aiki tsakanin kasashen biyu ya zama wajibi.

Dangane da alaka da tsakanin kasashen biyu kuwa ya bayyana cewa, alaka bata taba yankewa ba tsakanin Iran da Aljeriya, kuma a kullum alakar tana kara bunkasa a dukaknin bangarori.

Ya ce bababn abin da al’ummar musulmi ke bukata a halin yanzu shi en hadin kai da yin aiki tare a dukaknin bangarorin domin amfanin musulmia  duk inda suke.

 

3844565

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Aljeriya ، Iran ، alaka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: