IQNA

23:01 - September 27, 2019
Lambar Labari: 3484094
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Masar sun tsaurara matakai kan masu zanga-zagar adawa da shugaba Sisi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, an dauki kwararan matakan tsaroadukkanin biranan kasar Masar, domin takura matasan kasar masu zanga-zangar neman Al sisi ya sauka daga kan karagar mulki.

Dubban jami’an tsaron gwamnatin Kasar Masar suna ta sintiriaakan titunan biranan kasar, domin takura masu zanga-zangar adawa da Sisi.

Rahoton ya ce a yau Juma’a jami’an tsaro sun rika caje samari da suke nufa babban dandalin Al-tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira domin halartar babban gangami na nuna adawa da mulkin Abdulfattah Sisi, inda suke karbar wayoyi da kuma duba dukkanin shafukan zumunta na matasa.

Duk da daukar wadannan matakai, hakan bai hana dubban daruruwan matasa taruwa a birane daban-daban na kasar ba, domin yin kira ga Sisi day a gaggauta sauka daga kan shugabancin kasar, bayan bankado wata almundahana wadda yake da hannu dumu-dumu a cikinta.

Alosisi dai ya bayyana cewa ba shi da wata matsala idan an yi zanga-zanga a kansa, domin ya san mutanen Masar wayayyu ne, kuma za su kiyaye tsari.

3845198

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zanga-zangar ، adawa ، Masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: