IQNA

23:57 - September 29, 2019
Lambar Labari: 3484101
Bangaren kasa da kasa, sojojin Yemen tare da dakarun sa kai na kabilun kasar sun kame sojojin Saudiyya sama da dubu biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kakakin rundunar sojin kasar Yemen ya sanar da kaddamar da wani gagarumin farmaki mai taken “Nasrun Minallah” a kan dandazon sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korenta a Najran.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Brigadier General Yahya Sari ya bayyana cewa, dakarun kasar sun samu nasarar kaddamar da wani gagarumin farmaki mai taken “Nasrun Minallah” a kan dandazon sojojin Saudiyya da kuma ‘yan korenta daga kasashen ketare a Najran.

Ya ce an dauki tsawon watanni ana aiwatar da shirin wannan farmaki wanda ya gudana a cikin nasara, inda ya ce sun kama dubban sojoji a matsayin fursunonin yaki wadanda suka mika kansu da makamansu, bayan da dakarun na Yemen suka rutsa da su.

3845548

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yemen ، saudiyya ، hare-hare
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: