IQNA

22:07 - October 04, 2019
Lambar Labari: 3484117
Bangaren siyasa, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da bayani dangane da zanga-zangar da ke gudana a kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta bayyana takaici dangane da tashe-tashen hankulan da suka wakana a Iraki sakamakon zanga-zangar da wasu suka yi a  wasu biranan kasar.

Bayanin ya ce Iran tana imanin cewa wannan lamari ne da za a warware shi, sakamakon hikimar mahukunta da kuma manyan jagororin addini na kasar, tare da kiran al’ummar Iraki da kada su bari wasu daga waje su sa musu hannu su rusa kasarsu.

Haka nan kuma bayanin ya jaddada cewa dukkanin Iraniyawa da suke da niyyar tafiya zuwa taron arba’in za a jinkirta har zuwa lokacin da laurra suka daidaita.

 

3847000

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، gudana ، harkokin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: