IQNA

22:14 - October 04, 2019
Lambar Labari: 3484119
Bagaren kasa da kasa, dubban falastinawa sun gudanar ad gangami kamar yadda suka saba yia  kowace a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na ma’aikatar harkokin cikin gidan falastinu cewa, a yau ma dubban falastinawa sun gudanar da gangami kamar yadda suka saba yi a  kowace a Gaza domin neman hakkin falastinawa da aka kora su dawo kasarsu.

Wannan gangami dai ya samu halartar dubban mutane kamar kowace Juma’a, kuma sojojin Isra’ila masu tsaron iyakar Gaza sun bude wuta kan masu gangamin, inda suka kashe daya daga cikin falastinawam masu jerin gwanon lumana, tare da jikkata wasu.

Daya daga cikin jagororin falastinawa masu jagorantar gangamin ya bayyana cewa, kisa ba zai hana su ci gaba da neman hakkokinsu da aka haramta musu sama da shekau saba’in ba.

3847092

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: