IQNA

22:59 - October 05, 2019
Lambar Labari: 3484120
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani tsohon zane na tarihi na na kasar Turkiya da ke koma zuwa karni na 19.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, Usman Hamdi Bieg na ya zana wannan hoto tun a cikin karni na sha tara lokacin mulkin daular Usmaniya, wanda dakin ajiye kayan tarihi na Birtaniya ya saye shia  kan kudi dala miliyan 7 da dubu 400.

An zana wannan zane na yarinya tana karatun kur’ani tuna  cikin shekara ta 1880, wanda ke nuna ci gaban musulmi tun a wancan lokacin.

Julia Tagol wadda its ce shugabar dakin ajiye kayan tarihi na Birtaniya ta bayyana cewa, wannan zane na daya daga cikin abubuwan tarihi mafi muhimmanci da suke a jiye a wannan wuri.

Ta ce zane-zanen Bieg na daga cikin abubuwa masu daukar hankulan mutane a turai.

3847294

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: