Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, Usman Hamdi Bieg na ya zana wannan hoto tun a cikin karni na sha tara lokacin mulkin daular Usmaniya, wanda dakin ajiye kayan tarihi na Birtaniya ya saye shia kan kudi dala miliyan 7 da dubu 400.
An zana wannan zane na yarinya tana karatun kur’ani tuna cikin shekara ta 1880, wanda ke nuna ci gaban musulmi tun a wancan lokacin.
Julia Tagol wadda its ce shugabar dakin ajiye kayan tarihi na Birtaniya ta bayyana cewa, wannan zane na daya daga cikin abubuwan tarihi mafi muhimmanci da suke a jiye a wannan wuri.
Ta ce zane-zanen Bieg na daga cikin abubuwa masu daukar hankulan mutane a turai.