IQNA

23:02 - October 05, 2019
Lambar Labari: 3484122
Firayi ministan Malaysia ya tattauna shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wata tatatunawa tsakanin shugaban gwamnatin Malaysia Mahatir Muhammad, da kuma shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na Michelle Bachelet, ganawar ta gudana ne a birnin Potrajaya na kasar Malysia.

A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun dubi kan irin halin da musulmi ‘yan kabilar Rohingya suke ciki a kasarsu ta Myanmar, da kuam wurare da aka tsugunnar da su bayan da wasu daga cikinsu suka yi gudun zuwa kasashe makwafta.

Shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya Michelle Bachelet ta yaba da yadda kasar Malaysia take daukar auyin dubban ‘yan kabilar Rohingya da suke yin gudun hijira a kasar, inda ta ce ta ziyarce sansanonin da aka tsugunnan da ‘yan Rohingya a Malaysia, kuma ta yaba da yadda gwamnatin kasar take basu kulawa ta musamman.

Mahatir Muhammad ya jaddada cewa, nauyi da ya rataya kan al’ummomin duniya baki daya, da su taimaka wajen kawo karshen amwuyacin halin da aka jefa ‘yan kabilar ta Rohingya, tare da hakkokinsu da aka haramta musu a kasarsu.

Tun daga ranar 25 ga watan Agustan 2017 ne sojojin gwamnatin kasar Myanamra suka fara yin kisan kiyashi a kan musulmin Rohingya da ke yankin Rakhinakasar, inda aka kashe dubbai daga cikinsu wasu dubban daruruwa kuma suka tsere zuwa kasashe makwabta.

 

3847288

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: