IQNA

23:55 - October 08, 2019
Lambar Labari: 3484132
Bangaren kasa da kasa, Shugaban Iraki ya bukaci da a gudanar da tatatunawa tsakanin dukkanin al’ummar kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, a cikin jawabi da ya gabatar ga al’ummar kasar Iraki wamda dukkanin tashoshin kasar suka watsa kai tsaye, shugaban kasar Barham Saleh ya jaddada wajabcin gudanar da tattaunawa ta kasa baki daya.

Barham Saleh ya bayyana cewa, mutanen kasar Iraki suna da hakkin gudanar da zanga-zangar lumana domin bayyana ra’ayinsu ko korafe-korafensu ga mahukunta, kamar yadda ya rataya kan jami’an tsaro su ba su kariya.

Haka nan kuma ya bukaci bangaren shari’ar kasar da ya gudanar da bincike kan rasa rayukan da aka yi a  yayin zanga-zangar da wasu daga cikin Irakawa suka gudanar a  cikin makon da ya gabata, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Kamar yadda kuma ya bukaci a kafa kwamitin kwararru domin gudanar da sauye-sauye da za su taimaka waje warware matsaloli da mutane suke yin korafi a kansu.

 

 

 

3848245

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، Barham Saleh ، lumana
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: