IQNA

23:48 - October 09, 2019
Lambar Labari: 3484137
Bangaren kasa da kasa, a cikin wanann shekara yahudawa fiye da dubu 17 ne suka keta alfarmar masallacin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya naalto daga kamfanin dillancin labaran Palestine cewa, a cikin wannan wanann shekara ta muke ciki yahudawa fiye da dubu 17 ne suka keta alfarmar masallacin Quds mai alfarma.

Rahoton ya ce bias kididdigar da aka gudanar, daga farkon watan janairun farkon wanann shekara zuwa karshen watan Satumban da ya gabata, yahudawan sahyuniya 17878 ne suka kutsa kai a cikin masallacin quds.

A cikin watanni June zuwa Agusta kuwa, yahudawa 3410 ne suka kutsa kai a cikin masallacin, tare da keta alfarmarsa.

Rahoton ya ce a karon akrshe da yahudawan suka shiga cikin masalalcin, su fitar da musulmi 225 da suke cikin mallacin suna salla.

Yahudawa sukan kutsa kai cikin masallacin Aqsa a duk lokacin da suka ga dama tare da samun kariya daga jami’an tsaron Isra’ila.

 

3848850

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yahudawa ، quds ، aqsa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: